عن عائشة رضي الله عنها زوج النبي صلى الله عليه وسلم عن النبي صلى الله عليه وسلم قال:
«إِنَّ الرِّفْقَ لَا يَكُونُ فِي شَيْءٍ إِلَّا زَانَهُ، وَلَا يُنْزَعُ مِنْ شَيْءٍ إِلَّا شَانَهُ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2594]
المزيــد ...
Daga Nana Aisha Allah Ya yarda da ita, matar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare ta ta ce:
Lalle sassauci ba ya kasance wa a komai sai ya ƙara masa kyau, kuma ba a cire shi a komai sai ya aibanta shi.
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2594]
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayyana cewa rangwame da sauƙi da bi-sannu - sannu a magana da aiki suna ƙarawa abu kyau da cika da ƙaye, kuma nan ne ya fi cancanta mutum ya samu buƙatarsa.
Rashin sassauci yana aibanta lamura yana muzanta su, kuma yana hana mai hakan cimma buƙatarsa, in kuma ya samu, to, da baƙar wahala ne.