عن أبي صِرْمة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال:
«مَنْ ضَارَّ ضَارَّ اللهُ بِهِ، وَمَنْ شَاقَّ شَقَّ اللهُ عَلَيْهِ».
[حسن] - [رواه أبو داود والترمذي وابن ماجه وأحمد] - [سنن الترمذي: 1940]
المزيــد ...
Daga Abu Sirmah - Allah Ya yarda da shi - cewa manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Wanda ya cutar Allah Zai haɗa shi da sakamakon cutar, wanda ya tsananta Allah Zai haɗa shi da sakamakon tsanantawar".
[Hasan ne] - - [سنن الترمذي - 1940]
Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya yi gargaɗi game ga shigar da cuta ga musulmi, ko riskar da wahala a gareshi a kowane al'amari daga al'amauransa; a ransa ko a dukiyarsa ko a iyalansa, kuma cewa wanda ya aikata hakan Zai yi masa sakayya, Zaiyi masa uƙuba daga jinsin aikinsa.