عن أبي هريرة رضي الله عنه أَن النبيَّ صَلّى اللهُ عَلَيْهِ وسَلَّم قَالَ:
«الرَّجُلُ عَلَى دِينِ خَلِيلِهِ، فَلْيَنْظُر أَحَدُكُم مَنْ يُخَالِل».
[حسن] - [رواه أبو داود والترمذي وأحمد] - [سنن أبي داود: 4833]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Mutum yana kan Addinin abokinsa, saboda haka dayanku ya duba wanda zai yi abokantaka (da shi)".
[Hasan ne] - - [سنن أبي داود - 4833]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mutum yana kamanceceniya da abokinsa amintacce a rayuwarsa da kuma al'adarsa, kuma abokantaka tana tasiri a ɗabi'u da yanayi da tasarrufi, saboda haka ne ya nunar zuwa kyakkyawan zabin aboki; domin aboki yana shiryar da abokinsa akan imani da shiriya da alheri, kuma yana kasancewa taimako ga abokinsa.