عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الخُدْرِيِّ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«إِذَا سَمِعْتُمُ النِّدَاءَ، فَقُولُوا مِثْلَ مَا يَقُولُ المُؤَذِّنُ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 611]
المزيــد ...
Daga Abu Sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Idan kun ji kiran sallah, to ku fadi irin abinda ladani yake fada".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 611]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwadaitarwa akan amsa wa ladani a lokacin jinsa, hakan da mu fadi irin abinda yake fada, jumla da jumla, A yayin da ya yi kabbara sai mu yi kabbara a bayansa, a yayin da ya zo da shaida biyu, sai mu zo da su a bayansa. An togance lafazin: (Ku yi gaggawa zuwa sallah, ku yi gaggawa zuwa tsira) cewa za'a fada a bayansu: Babu dabara babu karfi sai ga Allah.