عن سعد بن أبي وقاص رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول:
«إِنَّ اللهَ يُحِبُّ الْعَبْدَ التَّقِيَّ الْغَنِيَّ الْخَفِيَّ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2965]
المزيــد ...
Daga Sa’ad Ɗan Abu Waƙƙas, Allah Ya yarda da shi, ya ce: Na ji Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa:
Lalle Allah Yana son bawa mai tsoronSa, wanda ya wadatu, mai ɓoye kansa.
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2965]
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayyana cewa Allah mabuwayi Yana son wasu daga cikin bayinsa.
Daga cikinsu akwai: Mai tsoron Allah wanda yake aikata abin da aka yi umarni, yake kuma nisantar hani.
Kuma yana son: Wanda ya wadatu ga barin mutane, ya yi riƙo da Allah maɗaukaki, ba ya waigawa ga wanin Allah.
Kuma yana son: Mai ɓoye kansa (wanda ba ya neman suna), mai tawalu’u, mai bauta ga Ubangijinsa, wanda ya shagaltu da abin da zai amfane shi, wanda bai damu da wani ya sanshi ba, ko wani ya yabe shi ba, ko ya burge ba.