+ -

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قال:
جَاءَ نَاسٌ مِنْ أَصْحَابِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَسَأَلُوهُ: إِنَّا نَجِدُ فِي أَنْفُسِنَا مَا يَتَعَاظَمُ أَحَدُنَا أَنْ يَتَكَلَّمَ بِهِ، قَالَ: «وَقَدْ وَجَدْتُمُوهُ؟» قَالُوا: نَعَمْ، قَالَ: «ذَاكَ صَرِيحُ الْإِيمَانِ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 132]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Wasu mutane daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sun zo wurisa sai suka tambaye shi: Mu muna ji a cikin zuciyarmu abinda da dayan mu zai fada to da yana da girma, ya ce: "Kuma hakika kun same shi ?" Suka ce: Eh, ya ce: "Wannan shi ne imani baro-baro".

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 132]

Bayani

Wasu jama'a daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sun zo sai suka tambaye shi game da abinda suke jinsa a cikin zuciyar su na manyan al'amuran da furta su zai girmama akansu saboda muninsu da kuma kyamarsu garesu. Sai tsira da aminci su tabbata agare shi ya ce: Lallai abinda kuke samunsa shi ne imani baro-baro da sakankancewar da zai kaiku ga hana abinda Shaidan yake jefawa acikin zuciya da kuma inkarinku ga furta shi, da girmama hakan acikin zukatan ku, kuma lallai cewa Shaidan ba ya samun dama a cikin zukatanku, sabanin wanda ya samu dama a zuciyarsa kuma bai samu abinda zai tunkude masa hakan ba.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية الطاجيكية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية Malagasy Italiyanci Oromo Kanadische Übersetzung Aserbaidschanisch الأوزبكية الأوكرانية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin raunin Shaidan ga ma'abota imani yayin da bai samu wani iko ba sai wasiwasi kawai.
  2. Rashin gasgatawa da karbar abinda yake zuwa a rai na wasiwasi, cewa su daga Shaidan ne.
  3. Wasiwasin Shaidan ba ya cutar da mumini, saidai ya nemi tsarin Allah daga wasiwasinsa, ya kuma hanu daga zarcewa a cikin hakan.
  4. Shiru ba ya kamata ga musulmi daga abinda yake rikice masa a al'amarin Addininsa, tamabaya game hakan ne ya kamata.
Kari