عن أنس بن مالك رضي الله عنه:
أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ لَا يَرُدُّ الطِّيبَ.
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 2582]
المزيــد ...
Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya yarda da shi
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance ba ya ƙin karɓar turare.
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 2582]
Ya kasance daga cikin karantarwar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba ya ƙin karɓar turare, yana karɓarsa domin yana da sauƙin ɗauka, kuma yana da ƙamshi.