عَنْ مُعَاذِ بْنِ جَبَلٍ رضي الله عنه:
أَنَّ رَسُولَ صَلَّى عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَخَذَ بِيَدِهِ، وَقَالَ: «يَا مُعَاذُ، وَاللَّهِ إِنِّي لَأُحِبُّكَ»، فَقَالَ: «أُوصِيكَ يَا مُعَاذُ لَا تَدَعَنَّ فِي دُبُرِ كُلِّ صَلَاةٍ تَقُولُ: اللَّهُمَّ أَعِنِّي عَلَى ذِكْرِكَ وَشُكْرِكَ وَحُسْنِ عِبَادَتِكَ».
[صحيح] - [رواه أبو داود والنسائي وأحمد] - [سنن أبي داود: 1522]
المزيــد ...
Daga Mu'az Bin Jabal -Allah Ya yarda da shi -:
Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe hannuna, sai ya ce: "Ya Mu'az, wallahi lallai ni ina sonka", sai ya ce: "Ina yi maka wasicci ya Mu'az bayan kowace sallah kada ka bar faɗin: Ya Allah Ka taimakeni akan ambatanKa da gode maKa da kyakkyawar ibadarKa".
[Ingantacce ne] - - [سنن أبي داود - 1522]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe hannun Mu'aza - Allah Ya yarda da shi -, sai ya ce masa: Wallahi lallai ni ina sonka, kuma ina yi maka wasicci ya Mu'az a ƙarshen kowace sallah kada kabar faɗin: (Ya Allah Ka taimakeni akan ambatanKa) a kowace magana da aikin da zai kusanto da ni zuwa biyayya, (da godiyarKa) ta hanyar samun ni'imomi da tunkuɗe masifu, (da kyakkyawar bautarKa) ta hanyar yin ikhlasi ga Allah da bin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.