+ -

عَن أَبِي أُمَامَةَ رضي الله عنه قَالَ: سَمِعْتَ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَخْطُبُ فِي حَجَّةِ الوَدَاعِ فَقَالَ:
«اتَّقُوا اللَّهَ رَبَّكُمْ، وَصَلُّوا خَمْسَكُمْ، وَصُومُوا شَهْرَكُمْ، وَأَدُّوا زَكَاةَ أَمْوَالِكُمْ، وَأَطِيعُوا ذَا أَمْرِكُمْ تَدْخُلُوا جَنَّةَ رَبِّكُمْ».

[صحيح] - [رواه الترمذي وأحمد] - [سنن الترمذي: 616]
المزيــد ...

Daga Abu Umama - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana huduba a hajjin bankwana sai ya ce:
"Ku ji tsoron Allah ku sallaci (sallolinku) biyar, ku azimci watanku (Ramadan) ku bada zakkar dukiyoyinku, ku bi shugabanku, zaku shiga aljannar Ubangijinku".

Ingantacce ne - Ibnu Hibban ne ya Rawaito shi

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi huduba a ranar Arfa, a hajjin bankwana, shekara ta goma daga hijira, an ambaceta da hakan; Domin cewa shi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi wa mutane bankwana a cikinta, ya umarci mutane gaba daya da su ji tsoron Ubangijinsu ta hanyar kamanta umarninSa da nisantar haninSa. Kuma su sallaci salloli biyar din da Allah - Mai girma da daukaka - Ya wajabta musu a yini da dare. Kuma Su azimci watan azimi (Ramadan). Kuma Su bada zakkar dukiyoyi ga wadanda suka cancanta kada su yi rowarta. Su kuma bi wadanda Allah Ya sanya su shgabanni akansu inba sabon Allah ba ne, wanda ya aikata wadannan abubuwan da aka ambata to ladansa shi ne shiga aljanna.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Swahili bushtu Asami السويدية الأمهرية الغوجاراتية القيرقيزية النيبالية اليوروبا الدرية الصومالية المالاجاشية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Wadannan ayyukan suna daga sabubban shiga aljanna.