+ -

عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«إِنَّ الدُّنْيَا حُلْوَةٌ خَضِرَةٌ، وَإِنَّ اللهَ مُسْتَخْلِفُكُمْ فِيهَا، فَيَنْظُرُ كَيْفَ تَعْمَلُونَ، فَاتَّقُوا الدُّنْيَا وَاتَّقُوا النِّسَاءَ، فَإِنَّ أَوَّلَ فِتْنَةِ بَنِي إِسْرَائِيلَ كَانَتْ فِي النِّسَاءِ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2742]
المزيــد ...

Daga Abu sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Lallai cewa duniya mai zakice koriya, kuma Allah Mai gadar daku ne a cikinta, sai ya duba yaya zaku yi aiki, don haka ku ji duniya kuma ku kiyayi mata, domin cewa farkon fitinar Banu Isra'ila ta kasance a mata ne".

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2742]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa duniya mai zakice a abubuwan zaki, kuma koriya a abin gani, sai mutum ya rudu da ita ya yi zari a cikinta ya kuma sanya ta mafi girman himmarsa. Kuma cewa Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka - ya sanya shashinmu zai maye gurbin sashi a wannan duniyar, dan ya duba ya zamu yi aiki, shin zamu tsaya da biyayyarSa, ko zamu saba maSa? Sannan ya ce: Ku kiyayi jin dadin duniya ya rudeku da kawarta, sai ya doraku akan barin abinda Allah Ya umarceku da shi, da kuma afkawa a cikin abinda ya haneku daga gareshi. Daga mafi girman abinda ya wajaba a kiyaya daga gare shi daga fitintinun duniya (su ne) mata, cewa ita ce farkon fitinar da Banu Isra'ila suka afka a cikinta.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung الولوف Aserbaidschanisch الأوكرانية الجورجية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwadaitarwa akan lazimtar tsoron Allah, da barin shagaltuwa da zahirin duniya da kawarta.
  2. Kiyayewa daga fitinuwa da mata, na kallo ko sakaci da cakuduwarsu da maza manisanta, ko wanin hakan.
  3. Fitinar mata tana daga mafi girman fitintinu a duniya.
  4. Wa'azantuwa da daukar izina daga al'ummun da suka gabata, abinda ya faru ga Banu isra'ila zai iya faruwa ga wasunsu.
  5. Fitinar mata idan ta kasance mata ce to ita zata iya dorawa mutum ciyarwar da ba zai iya ba, sai ta shagaltar da shi daga neman al'amuran Addini, ta kuma dora masa halaka a neman duniya, idan kuma manisanciya ce to fitinarta da rudar da maza ne da karkatar dasu daga gaskiya idan sun fita sun cakuda dasu, musanmama dai idan sun zama matsiraita masu shiga ta nuna tsiraici, wannan zai iya kaiwa zuwa afkawa a cikin zina a girmansa, to yana kamata ga mumini ya yi riko ga Allah, da kuma kwadayi gareShi don kubuta daga fitinarsu.