عن أنس رضي الله عنه قال:
كُنَّا عِنْدَ عُمَرَ فَقَالَ: «نُهِينَا عَنِ التَّكَلُّفِ».
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 7293]
المزيــد ...
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi ya ce:
Mun kasance a wurin Umar, sai ya ce: An hana mu ƙaƙale.
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 7293]
Umar Allah Ya yarda da shi yana ba da labarin Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana su yin abin da zai kawo wahala ba tare da wata buƙata a kan hakan ba, hakan magana ce ko aiki.