عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول:
«حَقُّ الْمُسْلِمِ عَلَى الْمُسْلِمِ خَمْسٌ: رَدُّ السَّلَامِ، وَعِيَادَةُ الْمَرِيضِ، وَاتِّبَاعُ الْجَنَائِزِ، وَإِجَابَةُ الدَّعْوَةِ، وَتَشْمِيتُ الْعَاطِسِ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 1240]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
"Hakkin musulmi akan musulmi guda biyar ne: Maida sallama, da gaida mara lafiya, da bin jana'iza, da amsa gayyata, da gaida mai atishawa".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1240]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana sashin hakkokin musulmi akan dan uwansa musulmi. Farkon wadannan hakkokin su ne maida sallama ga wanda ya yi maka sallama.
Hakki na biyu: Gaida mara lafiya da ziyartarsa.
Hakki na uku: Bin jana'iza daga gidansa zuwa wurin yin sallar, kuma zuwa makabarta har a binneta.
Hakki an hudu: Amsa gayyata idan ya gayyace shi zuwa walimar angwanci da wanin hakan.
Hakki na biyar: Gaida mai atishawa, shi ne ya ce masa idan ya godewa Allah: Allah ya yi maka rahama, sannana mai atishawar ya ce: Allah Ya shiryeku Ya gyara halayenku.