+ -

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المؤْمنينَ رَضيَ اللهُ عنها قَالَت:
قُلْتُ لِلنَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: حَسْبُكَ مِنْ صَفِيَّةَ كَذَا وَكَذَا، -قَالَ أَحدُ الرُّوَاةِ: تَعْنِي قَصِيرَةً- فَقَالَ: «لَقَدْ قُلْتِ كَلِمَةً لَوْ مُزِجَتْ بِمَاءِ الْبَحْرِ لَمَزَجَتْهُ» قَالَتْ: وَحَكَيْتُ لَهُ إِنْسَانًا، فَقَالَ: «مَا أُحِبُّ أَنِّي حَكَيْتُ إِنْسَانًا وَأَنَّ لِي كَذَا وَكَذَا».

[صحيح] - [رواه أبو داود والترمذي وأحمد] - [سنن أبي داود: 4875]
المزيــد ...

Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce:
Na cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ya isheka abu kaza da abu kaza daga Safiyya, - wani daga maruwaita ya ce: Tana nufin cewa ita gajera ce - sai ya ce: «Haƙiƙa kin faɗi kalmar da za'a cakuɗata da ruwan kogi da ta canza shi» ta ce: Kuma na kwaikwayi wani mutum gare shi , sai ya ce: «Bana son ace na kwaikwayi wani mutum koda kuwa (na karɓi) abu kaza da abu kaza».

[Ingantacce ne] - - [سنن أبي داود - 4875]

Bayani

Nana Aisha Uwar muminai A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ya isheka daga Safiyya - tana nufin Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - cewa daga cikin aibukanta na jiki ita gajera ce, sai ya ce: Haƙiƙa kin faɗi kalmar da da za'a cakuɗata da ruwan kogi da ta rinjaye shi ta canjashi ta kuma ɓata shi, ta ce: Kuma na aikata irin aikin wani mutum dan ɓata shi, sai Annabi - tsira da amincin Allsh su tabbata agare shi - ya ce: In ya faɗi aibinsa ba ya faranta mini rai, ko in kwaikwaye shi in aikata irin aikinsa ko in faɗi irin maganarsa ta fuskar tauyewa ko da kuwa an bani wani abu mai yawa na duniya akan haka.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Swahili Asami الأمهرية الهولندية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Gargaɗarwa da kuma tsoratarwa daga yi da mutum.
  2. Kwaikwayar yanayi da kwaikwayon mutane ta hanyar wulaƙantarwa da tauyewa yana daga yi da mutum wanda yake haramun ne.
  3. Siffanta aibuka na jiki wani yanki ne na yi da mutum.
  4. Alƙali ya ce: al-Mazju shi ne cakuɗawa da kuma canjawa ta hanyar cakuɗa waninsa da shi, ma'ana cewa wannan gibar da ace ta zama daga abinda za'a cakuɗa da ruwan kogi da ta canja shi daga yadda yake, duk da yawansa, to yaya kuwa da ace ayyuka ne kaɗan suka cakuɗa da shi.
  5. Bayanin abin da yake faruwa tsakanin ma'aurata na kishi.
  6. Rashin tabbatarwarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga wani aiki abin ƙi.
  7. Wulaƙantar da sha'anin duniya da abinda ke cikinta idan an haɗa da yardar Allah - Maɗaukakin sarki - da kuma rashin fushinSa.
  8. Musulunci Addini ne na ɗabi'u masu kyau, haƙiƙa an yi umarni da kiyaye mutunci kada a keta shi da magana ne ko da aiki; domin cewa shi yana daga abinda yake gadar da gaba da ƙiyayya tsakaknin musulmai.