عن عُمر بن أبي سلمة رضي الله عنه قال:
كُنْتُ غُلَامًا فِي حَجْرِ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، وَكَانَتْ يَدِي تَطِيشُ فِي الصَّحْفَةِ، فَقَالَ لِي رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «يَا غُلَامُ، سَمِّ اللهَ، وَكُلْ بِيَمِينِكَ، وَكُلْ مِمَّا يَلِيكَ» فَمَا زَالَتْ تِلْكَ طِعْمَتِي بَعْدُ.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 5376]
المزيــد ...
Daga Umar ɗan Abu Salama - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Na kasance yaro a kulawar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, hannuna ya kasance yana yawo a faranti, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce da ni: "Ya kai yaro, ka ambaci Allah, ka ci da damanka, ka ci abin da ke gabanka" hakan bai gushe ba shi ne irin cin abincina bayan nan.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 5376]
Umar Dan Abu Salama - Allah Ya yarda da su - ɗan matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - Ummu salamah - Allah Ya yarda da ita - yana ba da labari - (cewa) ya kasance ƙarƙashin renonsa da kulawarsa -, cewa ya kasance a tsakiyar cin abinci yana yawo da hannunsa asasannin ƙwarya (kwanon abin ci) don ya ɗauki abincin, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya sanar da shi ladubba uku daga ladubban cin abinci.
Na farkonsu: Faɗin "Da sunan Allah" a farkon ci.
Na biyunsu: Cin abinci da dama.
Na ukunsu: Cin abinci daga ɓangaren da yake kusa daga gare shi na abincin.