عن ابن عمر رضي الله عنهما أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال:
«إِذَا أَكَلَ أَحَدُكُمْ فَلْيَأْكُلْ بِيَمِينِهِ، وَإِذَا شَرِبَ فَلْيَشْرَبْ بِيَمِينِهِ، فَإِنَّ الشَّيْطَانَ يَأْكُلُ بِشِمَالِهِ، وَيَشْرَبُ بِشِمَالِهِ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2020]
المزيــد ...
Daga Dan Umar - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Idan ɗayanku zai ci; to, ya ci da damansa, idan zai sha; to, ya sha da damansa, domin cewa Shaiɗan yana ci da hagunsa, kuma yana sha da hagunsa".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2020]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana umarni cewa musulmi ya ci ya sha da hannunsa na dama, kuma yana hani daga ci da sha da hagu; domin cewa Shaiɗan yana ci kuma yana sha da shi (hannun hagu).