عَنْ جَرِيرٍ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«مَنْ يُحْرَمِ الرِّفْقَ يُحْرَمِ الْخَيْرَ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2592]
المزيــد ...
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda aka haramtawa sauƙi to an haramta masa alheri".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2592]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wanda aka haramtawa sauƙi to ba'a datar da shi ba a cikin al'amuran addini dana duniya haka da cikin abinda yake tasarrufi a cikinsa ga kansa, da kuma abinda yake tasarrufi a cikinsa tare da waninsa, to haƙiƙa an hana masa alheri gabaɗayansa.