عَن عَبْدِ اللَّهِ بنِ مَسْعُودٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: كُنَّا مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ:
«مَنِ اسْتَطَاعَ البَاءَةَ فَلْيَتَزَوَّجْ، فَإِنَّهُ أَغَضُّ لِلْبَصَرِ، وَأَحْصَنُ لِلْفَرْجِ، وَمَنْ لَمْ يَسْتَطِعْ فَعَلَيْهِ بِالصَّوْمِ، فَإِنَّهُ لَهُ وِجَاءٌ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 1905]
المزيــد ...
Daga Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce:
"Duk wanda yake da iko a cikinku to ya yi aure, domin cewa shi ne yafi rintse ido, kuma ya fi katange farji, wanda ba zai iya ba to na umarce shi da azimi, domin shi kariyane gare shi".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1905]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar da wanda yake da iko akan jima'i da ɗawainiyar aure da ya yi aure; domin cewa shi yafi kiyaye gani daga haram, kuma ya fi tsananin katange farjinsa, da kuma hana afkawa cikin alfasha, wanda ba zai iya ɗaukar ɗawainiyar aure ba alhali shi yana mai iko akan jima'i to ya yin azimi domin cewa shi yana yanke sha'awar farji da sharrin maniyyi.