1. Gida
  2. kashe kashe

Sabuntawa Cewa wani mutum ya zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya yi masa magana a akan wani al'amari, sai ya ce: Allah Ya so kaima ka so, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Zaka daidaitani da Allah ne? Ka ce : Allah Shi kadai ya so

عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما:

أَنَّ رَجُلًا أَتَى النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَكَلَّمَهُ فِي بَعْضِ الْأَمْرِ، فَقَالَ: مَا شَاءَ اللهُ وَشِئْتَ، فَقَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَجَعَلْتَنِي لِلَّهِ عَدْلًا؟ قُلْ: مَا شَاءَ اللهُ وَحْدَهُ».

Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su -
Cewa wani mutum ya zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya yi masa magana a akan wani al'amari, sai ya ce: Allah Ya so kaima ka so, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Zaka daidaitani da Allah ne? Ka ce : Allah Shi kadai ya so".

Sanadinsa Hasan ne Nasa'i cikin Alkubra da Ibnu Maja da Ahmad ne suka rawaito shi Sunanul Kubura Na Nasa'i - 10759

Bayani

Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya yi masa magana a kan wani al'amari nasa, sannan ya ce: "Allah Ya so kaima ka so", sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi masa inkarin wannan maganar, kuma ya nusar da shi cewa hada mashi'ar abin halitta akan mashi'ar Allah da Waw shirka ce karama, ba ya halatta ga musulmi ya furtata, sannan ya shiryar da shi magana ta gaskiya: "Allah Ya so Shi kadai", sai ya kadaita Allah a Son Sa, kada ya hada mashi'ar (ganin damar) wani akansa ta kowanne nau'i daga nau'o'in hadawa .

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Hani game da fadin: Allah Ya so kaima ka so, da abinda ke kama da shi daga abinda a cikinsa akwai hada mashi'ar (ganin damar) bawa akan mashi'ar Allah da Waw; Domin hakan shirka ce karama.
  2. Wajabcin hana abin ki.
  3. Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - hakika ya kiyaye janibin tauhidi, da toshe hanyoyin shirka.
  4. A lokacin hana abin ki yana da kyau nunawa wanda ake kira canjin da ya halatta, dan koyi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  5. Hadawa tsakanin fadinsa tsira da amincin Allah su tabbata agare shi a wannan Hadisin: "Allah Ya so Shi kadai", da fadinsa a daya Hadisin: "Ka ce Allah Ya so sannan ka so" cewa fadin mutum: "Allah Ya so sannan ka so" ya halatta, sai dai fadinsa: "Allah Ya so Shi kadai" yafi.
  6. Ya halatta ka ce : "Allah Ya so sannan ka so" sai dai abinda ya fi, fadin: "Allah Ya so Shi kadai".

Manufofin Fassarorin

58 Yare
EN English الإنجليزية
UR اردو الأوردية
ES Español الإسبانية
ID Indonesia الإندونيسية
UG ئۇيغۇرچە الأيغورية
BN বাংলা البنغالية
FR Français الفرنسية
TR Türkçe التركية
RU Русский الروسية
BS Bosanski البوسنية
SI සිංහල السنهالية
HI हिन्दी الهندية
ZH 中文 الصينية
FA فارسی الفارسية
VI Tiếng Việt الفيتنامية
TL Tagalog تجالوج
KU Kurdî الكردية
PT Português البرتغالية
ML മലയാളം المليالم
TE తెలుగు التلغو
SW Kiswahili السواحيلية
MY မြန်မာ البورمية
TH ไทย التايلندية
DE Deutsch الألمانية
PS پښتو بشتو
AS অসমীয়া الأسامية
SQ Shqip الألبانية
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча القيرقيزية
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá اليوروبا
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda الكينياروندا
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy المالاجاشية
IT Italiano الإيطالية
OM Oromoo الأورومو
KN ಕನ್ನಡ الكانادا
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan الأذربيجانية
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
KMR Kurmancî الكرمنجية
kashe kashe
  • . .