عن تميم الداري رضي الله عنه أن النبي صلى الله عليه وسلم قال:
«الدِّينُ النَّصِيحَةُ» قُلْنَا: لِمَنْ؟ قَالَ: «لِلهِ وَلِكِتَابِهِ وَلِرَسُولِهِ وَلِأَئِمَّةِ الْمُسْلِمِينَ وَعَامَّتِهِمْ».

Daga Tamim al-Dari - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Addini nasiha ne" Muka ce; ga wa? Ya ce; "Ga Allah da littafinsa, da Manzonsa, da shugabannin musulmai da dukkaninsu".

Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi Sahih Muslim - 55

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa addini a tsaye yake a kan ikhlasi da gaskiya, har a yi kamar yadda Allah Ya wajabta, cikakke ba tare da tawaya ko algus ba.
Sai aka cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Ga wa nasihar za ta kasance? sai ya ce:
Na farko: Nasiha ga Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya daukaka -: ta hanyar tsarkake aiki gare shi, da rashin haɗa wani da Shi, kuma mu yi imani da Rububiyyarsa da Uluhiyyarsa da sunayensa da siffofinsa, da girmama al'amarinsa, da kira zuwa imani da Shi.
Na biyu: Nasiha ga littafinsa shi ne Alƙur'ani mai girma: Shi ne cewa mu ƙudirce cewa shi zancensa ne, kuma ƙarshen littattafansa, kuma cewa shi mai shafewa ne ga dukkanin shari'o'i kafinsa, mu girmamashi, mu karantashi haƙiƙanin karantashi, mu yi aiki da muhkam ɗinsa, mu miƙa wuya ga abubuwa masu kamanceceniya a cikinsa, kuma mu kore tawilin masu karkacewa gareshi, mu wa'azantu da wa'azozinsa, da yaɗa ilimummukansa, da kira zuwa gareshi.
Na uku: Nasiha ga manzonsa (Annabi) muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Shi ne mu kudire cewa shi ne karshen manzanni, mu gasgatashi a cikin abin da ya zo da shi, mu kamanta umarninsa, mu nisanci haninsa, kuma kada mu bautawa Allah da komai sai abin da ya zo da shi, mu girmama haƙƙinsa, mu girmamashi, mu yaɗa da'awarsa, mu yaɗa shari'arsa, kuma mu kore tuhuma daga gareshi.
Na hudu: Nasiha ga shugabannin musulmai: Ta hanyar taimakonsu a kan gaskiya, da rashin jayayya da su a al'amari, da ji da biyayya garesu a cikin biyayya ga Allah.
Na biyar: Nasiha ga musulami: Ta hanyar kyautatawa zuwa garesu da kiransu, da kame cuta daga garesu, da son alheri garesu, da taimakekeniya tare da su a kan biyayya da tsoron Allah.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Umarni da nasiha ga kowa da kowa.
  2. Girman matsayin nasiha a addini.
  3. Addini ya ƙunshi ƙudirce-ƙudirce da maganganu da kuma ayyuka.
  4. Yana daga cikin nasiha tsarkake zuciya daga algus ga wanda aka yi wa nasihar da kuma nufin alheri gareshi.
  5. Kyakkyawar koyarwar Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayin da yake ambaton abu a dunkule sannan ya yi shi dalla-dalla.
  6. Farawa da mafi muhimmanci sannan mai bi masa, yayin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya fara da nasiha ga Allah, sannan littafinsa, sannan manzonsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sannan ga shugabannin musulmai, sannan kowa da kowansu.

Manufofin Fassarorin

69 Yare
EN English الإنجليزية
UR اردو الأوردية
ES Español الإسبانية
ID Indonesia الإندونيسية
UG ئۇيغۇرچە الأيغورية
BN বাংলা البنغالية
FR Français الفرنسية
TR Türkçe التركية
RU Русский الروسية
BS Bosanski البوسنية
SI සිංහල السنهالية
HI हिन्दी الهندية
ZH 中文 الصينية
FA فارسی الفارسية
VI Tiếng Việt الفيتنامية
TL Tagalog تجالوج
KU Kurdî الكردية
PT Português البرتغالية
ML മലയാളം المليالم
TE తెలుగు التلغو
SW Kiswahili السواحيلية
TA தமிழ் التاميلية
MY မြန်မာ البورمية
TH ไทย التايلندية
DE Deutsch الألمانية
JA 日本語 اليابانية
PS پښتو بشتو
AS অসমীয়া الأسامية
SQ Shqip الألبانية
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча القيرقيزية
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá اليوروبا
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda الكينياروندا
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy المالاجاشية
FF Fulfulde الفولانية
IT Italiano الإيطالية
OM Oromoo الأورومو
KN ಕನ್ನಡ الكانادا
WO Wolof الولوف
BG Български البلغارية
AZ Azərbaycan الأذربيجانية
EL Ελληνικά اليونانية
AK Akan الأكانية
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
LN Lingala اللينجالا
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
BM Bambara البامبارية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
DA Dansk الدنماركية
RN Kirundi الكيروندي
KMR Kurmancî الكرمنجية
MS Bahasa Melayu الملايو