+ -

عن جابر رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول:
«أَفْضَلُ الذِّكْرِ: لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، وَأَفْضَلُ الدُّعَاءِ: الْحَمْدُ لِلهِ».

[حسن] - [رواه الترمذي والنسائي في الكبرى وابن ماجه] - [سنن الترمذي: 3383]
المزيــد ...

Daga Jabir -Allah Ya yarda da shi- ya ce: Naji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa:
"Mafificin zikiri: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma mafificiyar addu'a: Godiya ta tabbata ga Allah".

[Hasan ne] - - [سنن الترمذي - 3383]

Bayani

Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana sanar da cewa mafificin zikiri: "La ilaha illal lahu" Ma'anarta babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma cewa mafificiyar addu'a godiya ta tabbata ga Allah; shi ne ikirari da cewa mai ni'imtarwa Shi ne Allah - tsarki ya tabbatar maSa -, wanda ya cancanci cikakkiyar siffa mai kyau.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصومالية الطاجيكية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية Malagasy Italiyanci Oromo Kanadische Übersetzung Aserbaidschanisch الأوزبكية الأوكرانية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwadaitarwa ga yawaita ambaton Allah da kalmar Tauhidi, da addu'a da godiya.