عن أبي موسى الأشعري رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال:
«مَنْ حَمَلَ عَلَيْنَا السِّلَاحَ فَلَيْسَ مِنَّا».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 7071]
المزيــد ...
Daga Abu Musa Al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:
"Wanda ya ɗaga makami a kammu, to, ba ya tare da mu"
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 7071]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana gargaɗarwa daga ɗaukar makami a kan musulmai, don tsorata su ko yi musu ƙwace, wanda ya aikata hakan ba tare da wani haƙƙi ba, to, haƙiƙa ya aikata babban laifi daga manyan laifuka, kuma ya cancanci wannan narkon mai tsanani.