عن أبي ذر رضي الله عنه أنه سمع النبي صلى الله عليه وسلم يقول: «لا يَرْمِي رَجُل رَجُلًا بِالفِسْقِ أو الكُفْر إلا ارْتَدَّتْ عليه، إن لم يَكُنْ صَاحبه كذلك».
[صحيح] - [رواه البخاري]
المزيــد ...
Daga Abu Zarr -Allah ya yarda da shi- cewa shi ya ce: naji Manzon Allah SAW yana cewa: "Kada wani Mutum ya jefi wani Mutum da Fasiqanci ko kafirci face sai ta dawo kansa, indai wanda aka jefa xin ba shi da ita"
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi]
Annabi SAW ya haramta Mutum ya ce da wani Mutum ya kai Fasiqi ko ya kai Kafiri; saboda indai wanda aka gayawa ba shi da shi, lallai kalmar zata dawo kan wanda ya faxe ta