عن عبد الله بن عمر رضي الله عنهما قال:
سَمِعَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رَجُلًا يَعِظُ أَخَاهُ فِي الْحَيَاءِ، فَقَالَ: «الْحَيَاءُ مِنَ الْإِيمَانِ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 36]
المزيــد ...
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce:
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ji wani mutum yana yi wa ɗan uwansa wa'azi game da kunya, sai ya ce: "Kunya tana daga imani".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 36]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ji wani mutum yana yi wa wani ɗan uwansa nasihar cewa ya bar yawan kunya! sai ya bayyana masa cewa kunya tana daga imani, kuma ba ta zuwa sai da alheri.
Kunya ɗabi'a ce da take sa aikata mai kyau da barin mummuna.