+ -

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم قَالَ:
«دَعُونِي مَا تَرَكْتُكُمْ، إِنَّمَا هَلَكَ مَنْ كَانَ قَبْلَكُمْ بِسُؤَالِهِمْ وَاخْتِلَافِهِمْ عَلَى أَنْبِيَائِهِمْ، فَإِذَا نَهَيْتُكُمْ عَنْ شَيْءٍ فَاجْتَنِبُوهُ، وَإِذَا أَمَرْتُكُمْ بِأَمْرٍ فَأْتُوا مِنْهُ مَا اسْتَطَعْتُمْ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 7288]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Ku barni a abinda na bar muku, kaɗai waɗanda ke gabaninku sun halaka ne da tambayarsu da kuma saɓawarsu ga annabawansu, idan na haneku daga wani abu to ku nuisance shi, idan na umarceku da wani abu to ku zo da shi daidai ikonku".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 7288]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci cewa hukunce-hukuncen shari'a sun rabu gida uku: Abinda aka yi shiru akan sa, da abubuwan da aka hana, da abubuwan da aka yi umarni.
Amma na farko: Shi ne wanda shari'a ta yi shiru akansa, ta yadda babu wani hukunci, sai kuma cewa asali a abubuwa rashin wajabci; amma a zamaninsa - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - to barin tambaya ga wani abu da bai afku ba yana wajaba dan tsoron kada a wajabta ko haramci ya sauka a kan shi, domin Allah Ya bar su ne dan rahama ga bayi. Amma bayan rasuwarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - idan tambayar ta kasance ta fuskar neman fatawa ce ko koyarwa ga abinda ake buƙatuwa a gare shi na al'amarin addini to ya halatta, kai an yi umarni da shi ma, idan kuma ta fuskar ta'annututi ce da ɗorawa kai to shi ne abinda ake nufi da barin tambaya daga gare shi a cikin wannan Hadisin; hakan domin cewa shi zai iya kaiwa zuwa kwatankwacin abinda ya afku ga Banu Isra'ila, dan an umarce su su yanka saniya da sun yanka kowacce irin saniya da sun aikata umarni, sai dai su sun tsananta sai aka tsananta musu.
Na biyu: Abubuwan da aka hana; su ne: Abinda ake bawa wanda ya bar shi lada, kuma ana yi wa wanda ya aikata shi uƙuba, to nisantarsu yana wajaba.
Na uku: Abubuwan da aka umarta; shi ne abinda ake bawa wanda ya aikata shi lada, kuma ana yi wa wanda ya bar shi uƙuba, to yana wajaba ya aikata shi gwargwadan iko.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tailand bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الدرية الصومالية Kinyarwanda الرومانية Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Abinda ya kamata a shagalta da mafi muhimmancin abinda ake buƙatuwa zuwa gare shi, da barin abin da ba'a buƙatuwa zuwa gare shi a wannan lokaci, da barin shagaltuwa da tambaya daga abinda bai afku ba.
  2. Haramcin tambayar da wataƙila ta kai zuwa ƙulle mas'aloli, da buɗe ƙofar shubuhohi masu kaiwa zuwa yawan saɓani.
  3. Umarni da barin dukkan abinda aka hana; domin babu wata wahala a barinsu, saboda haka hanin da aka ya yi zama gamamme.
  4. Umarni da aikata abinda aka yi umarni da shi gwargwadan iko; domin zai iya lizimtar da wahala ko a gajiya a aikata shi; saboda haka umarni da shi ya zama akan gwargwadan iko.
  5. Hani akan yawan tambaya, haƙiƙa malamai sun raba tambaya gida biyu: Ta ɗayansu: Wadda take kasancewa ta fuskar koyarwa ga abinda ake buƙatuwa zuwa gare shi na al'amarin addini, to wannan an yi umarni da ita, daga wannan nau'in tambayoyin sahabbai suke.
  6. Na biyu: Wadda ta kasance ta fuskar ta'annuti da ɗorawa kai to wannan ita ce wacce aka hana.
  7. Gargaɗin wannan al'ummar daga saɓawa annabinta, kamar yadda ya afku a cikin al’ummun da suka gabata.
  8. Yawan tambaya yana daga abinda ba'a buƙatuwa zuwa gare shi, kuma saɓawa annabawa sababi ne na halaka, musamman ma a cikin al'amuran da kaiwa gare su ba zai yi wu ba, misalin: Mas'alolin gaibun da babu wanda ya sansu sai Allah, da halayen ranar Alkiyama.
  9. Hana yin tambaya a mas'aloli masu tsanani, Auza'i ya ce: Lallai Allah idan Ya yi nufin haramtawa bawanSa albarkar ilimi sai Ya jefawa harshensa galaɗi mai yawa, haƙiƙa na gansu (su ne) mafi ƙarancin mutane a ilimi. Ibnu Wahab ya ce: Na ji Malik yana cewa: Gaddama a cikin ilimi tana tafiyar da hasken ilimi daga zuciyar mutum.