+ -

عَنْ عُثْمَانَ رضي الله عنه قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«مَا مِنَ امْرِئٍ مُسْلِمٍ تَحْضُرُهُ صَلَاةٌ مَكْتُوبَةٌ فَيُحْسِنُ وُضُوءَهَا وَخُشُوعَهَا وَرُكُوعَهَا، إِلَّا كَانَتْ كَفَّارَةً لِمَا قَبْلَهَا مِنَ الذُّنُوبِ، مَا لَمْ يُؤْتِ كَبِيرَةً، وَذَلِكَ الدَّهْرَ كُلَّهُ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 228]
المزيــد ...

Daga Usman -Allah Ya yarda da shi- ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
"Babu wani mutum musulmi da sallar farilla zata halarto shi, sai ya kyautata alwalarta da khushu'inta da ruku'inta, sai ta zama kaffara ga abinda ke gabaninta na zunubai, muddin dai bai aikata babban laifi ba, hakan a zamani ne gaba dayansa".

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 228]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa babu wani musulmin da lokacin sallar farilla zai shigo masa, sai ya kyautata alwalarta, ya cikata, sannan ya yi khushu'i a sallarsa ta inda zuciyarsa da gabbansa gaba dayansu zasu zama masu fuskantar Allah masu halarto girmansa, kuma ya cika ayyukan sallah kamar ruku'u da sujjada da waninsa, sai ta zama mai kankarewa ce ga abinda ke gabanta na kananan zunubai, muddin dai bai aikata babban laifi daga manyan laifuka ba, wannan falalar mai mikewa ce iya shudewar zamani kuma a kowacce sallah.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tailand bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung الولوف الأوكرانية الجورجية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Sallah mai kankare zunubai ita ce wacce bawa ya kyautata alwalarta, kuma ya yi ta yana mai khushu'i ya nufi yardar Allah - Madaukakin sarki - da ita.
  2. Falalar dawwama akan ibadu, kuma cewa su sababine na gafarta kananan zunubai.
  3. Falalar kyautata alwala, da kyautata sallah da khushu'i a cikinta.
  4. Muhimmancin nisantar manyan zunubai dan gafarta kananan zunubai.
  5. Manyan zunubai ba'a kankaresu sai da tuba.