عن أنس رضي الله عنه قال: كان أكثر دعاء النبي صلى الله عليه وسلم : «اللهم آتنا في الدنيا حسنة، وفي الآخرة حسنة، وقنا عذاب النار.
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Wannan fassarar tana bukatar Karin bita da gyaran yare.

An rawaito daga Anas -Allah ya yarda da shi- ya ce: "Ya Kasance mafi yawan Addu'ar Manzon Allah -Tsira da Amincin ALlah su tabbata a gare shi- "Ya Ubangijinmu ka bamu Mai kyau a cikin Duniya, kuma ka bamu mai kyau a Lahira kuma ka tsaremu Azabar Wuta"
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

Bayani

Annabi ya Kasance yana yin Addu'a da wannan Addu'ar, kuma yana yawaita yin Addu'a da ita saboda ta tare Ma'anoni baki dayansu na al-amarin duniya da Lahira, Mai a nan ita ce ni'ama, sai ya roki Alkaitin Duniya da lahira, da kuma kariya daga Wuta, saboda yana daga cikin Al-kairan duniya da lahira rokar kowane abun so da bukata, kuma daga mai kyau a Lahira Babbar ni'ama, wacce ita ce Yardar Allah da kuma shiga Al-jannar sa, amma kuma kariya daga Wuta saboda ita ce cikar ni'ama da kuma tafiyar tsoro da Bacin rai

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin