عن شداد بن أوس رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم : "سيد الاستغفار أن يقول العبد: اللهم أنت ربي لا إله إلا أنت خلقتني وأنا عبدك وأنا على عَهْدِكَ وَوَعْدِكَ ما اسْتَطَعْتُ أعوذ بك من شر ما صنعتُ أَبُوءُ لك بنعمتك عليَّ وأَبُوءُ لك بذنبي فَاغْفرْ لي فإنه لا يغفر الذنوب إلا أنت".
[صحيح] - [رواه البخاري]
المزيــد ...

Wannan fassarar tana bukatar Karin bita da gyaran yare.

An rawaito daga Shaddad Bn Aus -Allah ya yarda da shi- daga Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi: "Shugaban Istigfari shi ne kace: "Ya Ubangiji kai ne Ubangiji na kuma babau wani ubangijin Sai kai, Ka halicce ni kuma ni bawanka ne kuma ina kan Alkawarinka da nai maka da kuma Alkawarin ka da kaimun gwargwadon iko ina neman tsari da kai daga Sharrin abunda na aikata kuma ina furici da Ni'a,marka da kaimun kuma ina furuci da Zunubai na Saboda haka kayi mun gafara saboda babu mai yin gafarar zunubai sai kai"
Ingantacce ne - Buhari ne ya rawaito shi

Bayani

Annabi yana bamu Labari cewa lafazan Addu'a kamar su ne Shugaban Istigfari wanda ya ke Bawa zai ce: "Ya Ubangiji kai ne Ubangiji na kuma babu wani Ubangijin sai kai Kai ka Halicce ni kuma ni Bawanka ne kuma ina kan Al-kawarin da nai maka da wanda kayi mun gwargwadon iko na kuma ina neman tsarinka daga Sharrin abunda na aikata kuma ina furuci da Ni'amarka a gare ni kuma ina furuci da zunubina saboda haka ka gafarta mun saboda babu mai gafarta Zunubi sai kai" sai Bawa yayi Ikirari da da Tauhidi a farko, kuma cewa shi yana kan abunda yayi wa Allah Alkawari, na yin Imani da kuma biyayya gare shi, gwargwadon ikonsa, ba wai yadda ya kamata ga Allah ba da kuma ya cancanta a gare shi, domin Bawa ko yaya ya tsaya da yin ibada ba zai taba iya zuwa da duk abun da Allah ya Umarce shi da shi ba, ko kuma iya biyan wani wajibin godiyar Ni'ama da ta Wajaba akansa, sannan kuma ya dogara da shi da ya nemi kariyarsa, domin shi ne abun neman Kariyar da shi daga dukkan Sharrin abun da Bawa ya aikata, kuma ya Bawa ya tabbata cewa kuma ya yi Furuci gare shi da ni'amarsa a gare shi, kuma yana maida Al-hakin Zunubansa zuwa kansa hakana Sabonsa, sannan yana rokon Allah ya gafarta masa kuma ya sutuce shi daga Zunubai da sauran laifuffuka da Afuwarsa da kuma Rahamarsa, saboda babu Mai gafarta Zunubai sai shi Mai girma da Daukaka.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية الدرية
Manufofin Fassarorin