عن عبد الله بن مسعود رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «عليكم بالصدق، فإن الصدق يهدي إلى البِرِّ، وإن البر يهدي إلى الجنة، وما يزال الرجل يصدق ويَتَحَرَّى الصدق حتى يكتب عند الله صِدِّيقًا، وإياكم والكذب، فإن الكذب يهدي إلى الفجور، وإن الفجور يهدي إلى النار، وما يزال الرجل يكذب ويَتَحَرَّى الكذب حتى يكتب عند الله كَذَّابا»
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Wannan fassarar tana bukatar Karin bita da gyaran yare.

An rawaito daga Abdullahi Bn Mas'ud -Allah ya yarda da shi- ya ce: Maon Allah tisira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Na hore ku da gaskiya, saboda gaskiya tana shiryarwa zuiwa biyayya, kuma lallai biyayya tana siryarwa zuwa Al-janna, kuma Mutum ba ai gushe ba yana yin gaskiya kuma yana kirdadon Gaskiya har sai an rubuta shi a wajen Allah mai gaskiya, kuma na haneku da karya, saboda karya tana shiryarwa ne zuwa Fajirci, kuma Fajirci yana shiryarwa ne zuwa Wuta, kuma Mutum ba ai gushe yana karya kuma yana kirdadon Karya har sai an rubuta shi a wajen Allah"
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Annabi ya kwadaitar kan yin Gaskiya da kuma Lizimtar ta da kuma kokarin kirdadonta da bayanin Amfaninta da Karshenta mai kyau a duniya da Lahira, Saboda Gaskiya ita Asalin biyayya wanda shi ne Hanyar zuwa ga Al-janna, kuma Mutum ba zai lazamci Gaskiya ba sai an rubuta shi cikin Masu gaskiya a wajen Allah kuma wanna yana nuna kyakkyawan Karshe da kuma nuni zuwa cewa shi zai kasance Mai amintacciyar Makoma, kuma Annabi ya tsawatar daga barin Karya ya kuma bayyana cutarta da Shu'amancin Karshenta, saboda ita ce Asalin Fajirci wanda yake kai Mutum zuwa Wuta

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Kurdawa Portuguese Yaran Tamili
Manufofin Fassarorin