+ -

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«مَنْ صَامَ رَمَضَانَ إِيمَانًا وَاحْتِسَابًا غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِهِ»

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 38]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya azumci Ramadan yana mai imani da neman lada za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 38]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba da labari cewa wanda ya azumci watan Ramadan yana mai imani da Allah, yana mai gasgatawa da wajabcin azumin da abinda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yi tanadi na gwaggwaɓan ladaddaki da sakamako, yana mai nufin zatin Allah - Maɗauakakin sarki - da shi ba don riya ko jiyarwa ba, za'a gafarta masa zunubansa da suka shuɗe.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية الطاجيكية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy الفولانية Italiyanci Oromo Kanadische Übersetzung الولوف البلغارية Aserbaidschanisch الأوزبكية الأوكرانية الجورجية اللينجالا المقدونية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. FALALAR TSARKAKE NIYYA DA MUHIMMANCINSA A AZUMIN RAMADAN DA WANINSA NA AYYUKA NA GARI.