عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما:
أَنَّ رَجُلًا أَتَى النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَكَلَّمَهُ فِي بَعْضِ الْأَمْرِ، فَقَالَ: مَا شَاءَ اللهُ وَشِئْتَ، فَقَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَجَعَلْتَنِي لِلَّهِ عَدْلًا؟ قُلْ: مَا شَاءَ اللهُ وَحْدَهُ».
[إسناده حسن] - [رواه ابن ماجه والنسائي في الكبرى وأحمد] - [السنن الكبرى للنسائي: 10759]
المزيــد ...
Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su -
Cewa wani mutum ya zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya yi masa magana a akan wani al'amari, sai ya ce: Allah Ya so kaima ka so, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Zaka daidaitani da Allah ne? Ka ce : Allah Shi kadai ya so".
[Sanadi nsa Hasan ne] - - [السنن الكبرى للنسائي - 10759]
Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya yi masa magana a kan wani al'amari nasa, sannan ya ce: "Allah Ya so kaima ka so", sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi masa inkarin wannan maganar, kuma ya nusar da shi cewa hada mashi'ar abin halitta akan mashi'ar Allah da Waw shirka ce karama, ba ya halatta ga musulmi ya furtata, sannan ya shiryar da shi magana ta gaskiya: "Allah Ya so Shi kadai", sai ya kadaita Allah a Son Sa, kada ya hada mashi'ar (ganin damar) wani akansa ta kowanne nau'i daga nau'o'in hadawa .