عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«إِنَّ الدِّينَ يُسْرٌ، وَلَنْ يُشَادَّ الدِّينَ أَحَدٌ إِلَّا غَلَبَهُ، فَسَدِّدُوا وَقَارِبُوا، وَأَبْشِرُوا، وَاسْتَعِينُوا بِالْغَدْوَةِ وَالرَّوْحَةِ وَشَيْءٍ مِنَ الدُّلْجَةِ».
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 39]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Lallai Addini mai sauƙi ne, babu wanda zai tsananta cikinsa face sai ya rinjaye shi, saboda haka ku daidaita ku kusanto, ku yi bushara, ku nemi taimakon Allah da jijjifi da kuma yammaci da wani abu na duhun dare".
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 39]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa Addinin Musulunci an gina shi akan sauƙaƙawa da sauƙi a dukkan sha’aninsa, sauƙi yana ƙarfafa a lokacin samun gajiyawa da buƙata, kuma domin cewa tsanantawa a ayyuka na Addini da barin sauƙi ƙarshensa shi ne gajiyawa da yankewa daga barin aiki gabaɗayansa ko wani daga ciki. A Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan tsakatsakiya ba tare da zirfafawa ba; kada bawa ya taƙaita a cikin abinda aka umarce shi da shi, kuma kada ya ɗorawa kansa abinda ba zai iya ba, idan ya gajiya daga cikakken aiki to ya yi aiki akan abinda yake kusa da hakan.
Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi bushara da sakamako mai yawa akan dawwamammen aiki koda kadan ne ga wanda ya gajiya daga aiki cikakke; domin kasawa idan bata kasance daga aikinsa ba to bata lazimtar tauye ladansa.
Yayin da cewa duniya a haƙiƙa gidan tafiya ce da tashi zuwa lahira sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi umarni da neman taimako akan dawwama akan ibada ta hanyar yinta a cikin lokuta uku masu sa nishaɗantarwa:
Na farko: Jijjifi: Da tafiya a farkon yini; tsakanin sallar Asuba da hudowar rana.
Na biyu: Yammaci: Da tafiya bayan karkacewar rana.
Na uku: Duhun dare: Da tafiyar dare gabaɗayansa ko sashinsa, domin cewa aikin dare yafi wahala akan aikin rana sai aka yi umarni da sashinsa da faɗinsa: Da wani abu daga duhun dare.