عَنْ عَبْدِ الرَّحْمَنِ بْنِ سَمُرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«لَا تَحْلِفُوا بِالطَّوَاغِي، وَلَا بِآبَائِكُمْ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 1648]
المزيــد ...
Daga Abdurrahman ɗan Samura - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Kada ku yi rantsuwa da ɗagutai, ko da iyayenku".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1648]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana hani daga rantsuwa da ɗawagitai, jam'ine na dagutu, sune gumakan da mushrikai suke bauta musu koma bayan Allah, sune sababin shisshiginsu da kafircinsu, kuma tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana yin hani daga rantsuwa da iyaye; inda ya kasance daga al'adar larabawa a Jahiliyya shi ne su yi rantsuwa da iyayensu dan alfahari da girmamawa.