+ -

عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«يَقُولُ اللَّهُ تَعَالَى لِأَهْوَنِ أَهْلِ النَّارِ عَذَابًا يَوْمَ القِيَامَةِ: لَوْ أَنَّ لَكَ مَا فِي الأَرْضِ مِنْ شَيْءٍ أَكُنْتَ تَفْتَدِي بِهِ؟ فَيَقُولُ: نَعَمْ، فَيَقُولُ: أَرَدْتُ مِنْكَ أَهْوَنَ مِنْ هَذَا، وَأَنْتَ فِي صُلْبِ آدَمَ: أَلّاَ تُشْرِكَ بِي شَيْئًا، فَأَبَيْتَ إِلَّا أَنْ تُشْرِكَ بِي».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 6557]
المزيــد ...

Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
Allah - Maɗaukakin sarki - Zai cewa mafi ƙanƙantar 'yan wuta azaba a ranar lahira: Shin da ace duk abinda ke cikin ƙasa naka ne shin zaka fanshi kanka da shi? Sai ya ce: Eh, Sai ya ce: Na so ƙasa da hakan daga gareka alhali kai kana cikin tsatson (annabi) Adam: Kada ka ka yi min tarayya da wani abu, sai kaƙi sai dai ka yi shirka daNi".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6557]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Zai cewa mafi ƙanƙantar 'yan wuta a zaba bayan shigarta: Da ace duniya da abinda ke cikinta nakane shin zaka fanshi kanka da ita daga wannan azabar? Sai ya ce: Eh, Sai Allah Ya ce: Haƙiƙa Na nema daga gareka kuma Na umarceka da mafi sauƙi daga hakan lokacin da aka karɓi alƙawari gareka alhali kai kana cikin tsatson (annabi) Adam da kada ka yi shirka daNi da wani abu; sai kaƙi lokacin da Na fitar da kai zuwa duniya sai dai shirka.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Yaran Tailand bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية الرومانية Malagasy
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Falalar Tauhidi da sauƙin aiki da shi.
  2. Haɗarin shirka da Allah - Maɗaukakin sarki - da ƙarshenta.
  3. Allah Ya riƙi alƙawari ga 'ya'yan Adam a bayan babansu Adam da rashin yin shirka.
  4. GargaɗI akan shirka kuma cewa duniya gabaɗayanta ba zata wadatar da kafiri da komai ba a ranar lahira.