+ -

عَنْ عَدِيِّ بْنِ حَاتِمٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«مَا مِنْكُمْ مِنْ أَحَدٍ إِلَّا سَيُكَلِّمُهُ اللهُ، لَيْسَ بَيْنَهُ وَبَيْنَهُ تُرْجُمَانٌ، فَيَنْظُرُ أَيْمَنَ مِنْهُ فَلَا يَرَى إِلَّا مَا قَدَّمَ، وَيَنْظُرُ أَشْأَمَ مِنْهُ فَلَا يَرَى إِلَّا مَا قَدَّمَ، وَيَنْظُرُ بَيْنَ يَدَيْهِ فَلَا يَرَى إِلَّا النَّارَ تِلْقَاءَ وَجْهِهِ، فَاتَّقُوا النَّارَ وَلَوْ بِشِقِّ تَمْرَةٍ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 1016]
المزيــد ...

Daga Adiyyu ɗan Hatim - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira daa mincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
‘’Babu wani daga cikinku face sai Allah ya yi magana da shi, babu wani tafinta a tsakaninsu, sai ya duba zuwa daman sa ba zai ga komai ba face abinda ya aikata, sai ya yi duba zuwa hagunsa shima ba zai ga komai ba face abinda ya aikata, sai ya yi duba zuwa gabansa ba zai ga komai ba sai wuta wajen fuskarsa, to ku ji tsoron wuta ko da kuwa da gutsiren dabino ne".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1016]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa dukkan mumini zai tsaya a gaban Allah a ranar lahira shi kaɗai, kuma cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Zai yi magana da shi ba tare da wani wasiɗa ba, kuma babu wani tafinta a tsakaninsu wanda zai fassara zancen, sai ya yi duba ɓangaren dama da hagu saboda tsananin firgici, wataƙila zai samu hanyar da zai gudu a cikinta dan ya tsira daga wutar dake gabansa. Idan ya yi duba a ɓangaren da ke damansa ba zai ga komai ba sai abinda ya aikata na aiki na gari Idan ya yi duba a hagunsa ba zai ga komai ba sai abinda ya gabatar na mummunan aiki, idan ya duba gabansa ba zai ga komai ba sai wuta, kuma babu abinda zaisa shi kauce mata dan babu makawa daga wucewa akan siraɗi. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ku sanya kariya tsakaninku da wuta da sadaka da aiki na gari, koda da wani sassauƙan abu ne kamar rabin dabino.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tailand bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية الصربية الرومانية Malagasy
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwaɗaitarwa akan sadaka koda dan kadan ne, da ɗabi'antuwa da ɗabi'u ababen yabo, da mu'amala da sauƙi da tausasan zance.
  2. Kusancin Allah - Maɗaukakin sarki - ga bawanSa ranar lahira, dan babu wani shamaki ko wasiɗa ko tafinta a tsakaninsu, to mumini ya kiyayi saɓawa umarnin Ubangijinsa.
  3. Yana kamata ga mutum kada ya wulaƙanta abinda zai yi sadaka da shi koda ƙarami ne, domin shi kariya ne daga wuta.
Kari