«لَا يُؤْمِنُ أَحَدُكُمْ حَتَّى أَكُونَ أَحَبَّ إِلَيْهِ مِنْ وَالِدِهِ وَوَلَدِهِ وَالنَّاسِ أَجْمَعِينَ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 15]
المزيــد ...
An karbo daga Anas Allah Ya yarda da shi, ya ce: Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:
Imanin ɗayanku ba ya cika har sai na kasance mafi soyuwa a gare shi sama da babansa da ‘ya’yansa da mutane bakiɗaya.
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba mu labarin Musulmi ba zai kasance mai cikakken imani ba har sai ya gabatar da son Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a kan son babarsa da babansa da ɗansa da ‘yarsa da mutane bakiɗaya, wannan soyayya kuwa tana hukunta yi masa biyayya da taimaka masa da kuma barin saɓa masa.