عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«كُلُّ أُمَّتِي مُعَافًى إِلَّا المُجَاهِرِينَ، وَإِنَّ مِنَ المُجَاهَرَةِ أَنْ يَعْمَلَ الرَّجُلُ بِاللَّيْلِ عَمَلًا، ثُمَّ يُصْبِحَ وَقَدْ سَتَرَهُ اللَّهُ عَلَيْهِ، فَيَقُولَ: يَا فُلاَنُ، عَمِلْتُ البَارِحَةَ كَذَا وَكَذَا، وَقَدْ بَاتَ يَسْتُرُهُ رَبُّهُ، وَيُصْبِحُ يَكْشِفُ سِتْرَ اللَّهِ عَنْهُ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 6069]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
"Duk al'ummata an yafe musu sai masu bayyanarwa, kuma yana daga bayyanarwa mutum ya aikata wani aiki (mummuna) da daddare, sannan ya wayi gari Allah Ya rufa masa asiri, sai ya ce: Ya (ya falalarsa kansa) wane, jiya da daddare na aikata kaza da kaza, alhali ya kwana Uabangijinsa Ya rufa masa asiri, shi kuma ya wayi gari yana tona asirin da Allah Ya rufa masa".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6069]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa musulmi mai laifi ana yi masa kwadayin afuwar Allah da gafararSa, sai mai bayyanar da sabo dan alfahari da rashin kunya, to ba ya cancantar afuwa; ta inda yake aikata laifi da daddare, sannan ya wayi gari alhali Allah Ya rufa masa asiri, sai ya zantar da waninsa da cewa shi ya aikata sabo kaza jiya, ya kwana Ubangijinsa Ya rufa masa asiri, shi kuma ya wayi gari yana tona asirin da Allah Ya rufa masa!!