+ -

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«لَا تَصْحَبُ الْمَلَائِكَةُ رُفْقَةً فِيهَا كَلْبٌ وَلَا جَرَسٌ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2113]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce:
"Mala'iku ba sa tafiya da ayarin da a cikinsa akwai kare ko ƙararrawa".

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2113]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Mala'iku ba sa tafiya a ayari a atare dasu akwai kare, ko ƙararraar da ake ratayawa a wuyan dabbobi, sai ya fara kara idan an dabbar na tafiya.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tailand bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية التشيكية Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung الولوف
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Hani daga daukar karnuka da tafiya da su, in banda karen farauta ko na gadi.
  2. Mala'iku wadanda ba sa tafiya da (karnuka da kararrawa) su ne Mala'ikun rahama, amma masu rubuta ayyukan bayi to su ba sa rabuwa da bayi a zamansu da tafiye-tafiyensu.
  3. Hani daga ƙararrawa; Domin cewa ita garayace daga garayoyin shaidan, kuma a cikinta akwai kamanceceniya da gangar kiristoci.
  4. Ya wajaba akan musulmi ya yi kwadayi akan nisanta da dukkanin abinda sha'aninsa shi ne nisantar da mala'iku daga gare shi.