عَنْ أَبِي طَلْحَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«لاَ تَدْخُلُ المَلاَئِكَةُ بَيْتًا فِيهِ كَلْبٌ وَلاَ صُورَةٌ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 3322]
المزيــد ...
Daga Abu Ɗalha - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Mala'iku ba sa shiga gidan da yake akwai kare ko hoto a cikinsa".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 3322]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mala'ikun rahama ba sa shiga gidan da a cikinsa akwai kare ko hoton masu rayuka; Hakan cewa hoton abinda yake da rai: Saɓo ne mai muni, kuma a cikinsa akwai kamanceceniya da halittar Allah, kuma hanya ce daga hanyoyin shirka, wasu daga cikinsu hoton abinda ake bautawa ne koma bayan Allah. Amma sababin hanuwarsu daga (shiga) gidan da a cikinsa akwai kare: Saboda yadda yake yawan cin najasa, kuma sashinsu an ambace shi Shaiɗan; mala'iku kishiyotin shaiɗanu ne, saboda munin warin kare; mala'iku suna ƙin mummunan wari, kuma su (karnuka) an yi hani daga kiwonsu; sai aka yi wa mai riƙonsu ukuba da haramcin shigar mala'ikun rahama gidansa, da sallarsu a cikinsa, da nema masa gafara, da sa albarkarsu gare shi da kuma cikin gidansa, da tunkuɗewarsu cutar Shaiɗan daga gare shi .