عَنْ عَلِيٍّ رضي الله عنه قَالَ:

كُنْتُ رَجُلًا مَذَّاءً وَكُنْتُ أَسْتَحْيِي أَنْ أَسْأَلَ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لِمَكَانِ ابْنَتِهِ فَأَمَرْتُ الْمِقْدَادَ بْنَ الْأَسْوَدِ فَسَأَلَهُ فَقَالَ: «يَغْسِلُ ذَكَرَهُ وَيَتَوَضَّأُ». وَلِلبُخَاريِّ: فَقَالَ: «تَوَضَّأْ وَاغْسِلْ ذَكَرَكَ».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Aliyu Dan Abi Dalib Allah ya yarda s da shi yace: (Na kasance mutum mai yawan yin mazi, sai naji kunyar tambayar Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gareshi saboda matsayin y'arsa a waje na, sai na uamrci Mikdad Dan Aswad, ya tambaye shi, sai Annabi yace: Ya wanke Azzakarinsa, ya yi alwalla A wata ruwayar ta Buhari ((wanke Azzakarinka ka yi alwalla)) A wata ruwaya ta Muslim (( yi alwalla ka wanke gabanka))
Ingantacce ne - Buhari ne ya rawaito shi

Bayani

Aliyu Dan Abu Dalib Allah ya yarda da shi: yace Na kasance mutum mai yawan yin mazi, Na kasance ina yin wanka duk lokacin da na yi mazi, har ya zama wankan yana yi min wahalar yi; Don Na zaci hukuncinsa iri daya ne dana mani, sai Naso in tabbatar da hukuncinsa ,Naso tambayar Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi, kuma tambayar ta shafi al'aura ne, sannan 'yarsa a karkshi na take, sai Naji kunyar tambayarsa, sai na sa Mikdad Allah ya yarda da shi ya tambaye shi, sai ya tambaye shi, sai Annabi yace: idan mazi ya fito masa sai ya wanke gabansa har ya gusar da shi ta hanyar wanke shi da ruwa, kuma sai yayi alwala saboda kasancewarsa daga daya daga mafita biyu ya fito, duk abin da ya fito daga daya g daga cikinsu ya warware alwalla, ta haka ne Tsira da aminci ya shiryar da mai tambayar da wannan cikakken jawabi da umarni na shari'a da lafiya.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Yaran Tamili Yaran Tailand bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية الدرية
Manufofin Fassarorin

Ma"anonin Kalmomi