1. Gida
  2. kashe kashe

Sabuntawa Wanka ranar Juma'a wajibi ne akan kowanne baligi, kuma ya yi asuwaki, ya shafa tirare in ya samu

عَنْ عَمْرِو بْنُ سُلَيْمٍ الأَنْصَارِيُّ قَالَ: أَشْهَدُ عَلَى أَبِي سَعِيدٍ قَالَ: أَشْهَدُ عَلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:

«الغُسْلُ يَوْمَ الجُمُعَةِ وَاجِبٌ عَلَى كُلِّ مُحْتَلِمٍ، وَأَنْ يَسْتَنَّ، وَأَنْ يَمَسَّ طِيبًا إِنْ وَجَدَ».

Daga Amr Dan Sulaim Al-Ansari ya ce: Na shaida Abu sa'id ya ce: Na shaida Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Wanka ranar Juma'a wajibi ne akan kowanne baligi, kuma ya yi asuwaki, ya shafa tirare in ya samu".

الملاحظة
عرفنا ان الاسلام دينا جميلا
النص المقترح لا يوجد...
الملاحظة
عدوا خرجو داكشي علاش بحثو الناس
النص المقترح مالةن

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 880

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanka ranar Juma'a abu ne mai karfi kamar wajibi a hakkin kowanne namiji baligi daga musulmai daga wanda juma'a ta wajaba akansa, kuma ya tsaftace hakoransa da asuwaki da makancinsa, ya kuma shafa tirare da kowanne irin tirare mai kanshi.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Karfafar mustahabbancin wanka ranar Juma'a akan kowanne mutum musulmi baligi.
  2. Tsafta da kawar da wari mara kyau abin nema ne a shari'a ga kowanne musulmi.
  3. Girmama ranar Juma'a, da yin tanadi saboda ita.
  4. Karfafa mustahabbancin asuwaki a Juma'a.
  5. Anso Shafa tirare da kowanne irin tirare mai ƙanshi kafin tafiya Juma'a.
  6. Mace idan ta fita daga gidanta dan sallah ko waninta, to tirare ba ya halatta gareta; Dan nunin sunna akan haramcin hakan.
  7. Wanda ya isa mafarki shi ne baligi, balaga tana faruwa ne da wasu alamomi. Uku daga ciki mace da namiji suna tarayya a cikinsu, su ne: Na farko: Cikar shekara goma sha biyar. Na biyu: Idan gashi mai kauri ya tsiro a gefen farji. Na uku: Zubar maniyyi ta hanyar mafarki ko ta hanyar sha'awa koda ba tare da mafarki ba. Amma alama ta hudu to ita ce take kebantar mace, ita ce kuwa: Al’ada, idan mace ta yi al’ada to ta zama baliga.

Manufofin Fassarorin

58 Yare
EN English الإنجليزية
UR اردو الأوردية
ES Español الإسبانية
ID Indonesia الإندونيسية
UG ئۇيغۇرچە الأيغورية
BN বাংলা البنغالية
FR Français الفرنسية
TR Türkçe التركية
RU Русский الروسية
BS Bosanski البوسنية
SI සිංහල السنهالية
HI हिन्दी الهندية
ZH 中文 الصينية
FA فارسی الفارسية
VI Tiếng Việt الفيتنامية
TL Tagalog تجالوج
KU Kurdî الكردية
PT Português البرتغالية
ML മലയാളം المليالم
TE తెలుగు التلغو
SW Kiswahili السواحيلية
MY မြန်မာ البورمية
TH ไทย التايلندية
DE Deutsch الألمانية
PS پښتو بشتو
AS অসমীয়া الأسامية
SQ Shqip الألبانية
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча القيرقيزية
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá اليوروبا
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda الكينياروندا
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy المالاجاشية
IT Italiano الإيطالية
OM Oromoo الأورومو
KN ಕನ್ನಡ الكانادا
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan الأذربيجانية
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
KMR Kurmancî الكرمنجية
kashe kashe