عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«مَنْ حَلَفَ فَقَالَ فِي حَلِفِهِ: وَاللَّاتِ وَالعُزَّى، فَلْيَقُلْ: لاَ إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، وَمَنْ قَالَ لِصَاحِبِهِ: تَعَالَ أُقَامِرْكَ، فَلْيَتَصَدَّقْ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 4860]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Wanda ya rantse sai ya ce a cikin rantsuwarsa: Na rantse da Lata da Uzza, to ya ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, wanda ya ce wa abokinsa: Zo mu yi caca tare, to ya yi sadaka".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 4860]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana gargaɗi akan rantsuwa da wanin Allah; inda mumini ba ya rantsuwa sai da Allah kadai, kuma yana bada labarin cewa wanda ya yi rantsuwa da wanin Allah; kamar wanda ya yi rantsuwa ga misali da: Lata da Uzza - su biyun gumaka ne da ake bauta musu a lokacin Jahiliyya kafin Musulunci - to ya wajaba akansa ya ce yana mai riskar abin da ya fada da kansa: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, dan kuɓuta daga shirka, da kaffara daga wannan rantsuwar tasa.
Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bada labarin cewa wanda ya ce wa abokinsa: Zo mu yi wasan caca, - ita ce mutum ko sama da haka su yi rinjayeyeniya akan wata dukiyar da wani zai ɗauka a tsakaninsu, kuma kowanne daya daga cikinsu ba ya zama haka kodai yaci riba a cikinta ko kuma ya faɗi -; to an so ya yi sadaka da wani abu dan kaffara daga abinda ya yi kira zuwa gare shi.