+ -

عَنْ سَعْدِ بْنِ أَبِي وَقَّاصٍ رضي الله عنه عَنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّهُ قَالَ:
«مَنْ قَالَ حِينَ يَسْمَعُ الْمُؤَذِّنَ أَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، وَأَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ، رَضِيتُ بِاللهِ رَبًّا وَبِمُحَمَّدٍ رَسُولًا، وَبِالْإِسْلَامِ دِينًا، غُفِرَ لَهُ ذَنْبُهُ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 386]
المزيــد ...

Daga sa'ad Dan Abu Wakkas - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya ce:
"Wanda ya ce lokacin da ya ji mai kiran sallah: Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai, baShi da abokin tarayya, kuma cewa (Annabi) Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, na yadda da Allah Shi ne Ubangiji kuma (Annabi) Muhammad Manzo ne, kuma Musulunci shi ne Addini. Za’a gafarta masa zunubinsa".

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 386]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya ce lokacin da ya ji mai kiran sallah "Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai baShi da abokin tarayya" wato: Ina tabbatarwa ina bada labarin cewa babu wani abin bautawa da agskiya sai Allah, kuma dukkan wani abin bauta wanda ba shi ba to shi karya ne, "Kuma cewa (Annabi) Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne" wato: shi bawa ne ba'a bauta masa, kuma Manzone ba ya karya, "Na yarda da Allah Shi ne Ubangiji" wato: Da RububiyyarSa da UluuhiyyarSa da sunayenSa da siffofinsa, "Da (Annabi) Muhammad shi ne Manzo" wato: Da dukkanin abinda aka aiko shi da shi, kuma ya isar da shi garemu, "Da Musulunci" wato: Da dukkanin hukunce-hukuncen Musulunci na umarni da hani, "Addini" wato: A kudircewa da aikatawa, "Za'a gafarta masa zunubinsa" wato: kananunsu.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tailand bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية التشيكية Malagasy Oromo
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Maimaita wannan addu'ar a lokacin jin kiran sallah yana daga masu kankare zunubai.