عَنِ أَبِي مُوسَى رضي الله عنه، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّهُ كَانَ يَدْعُو بِهَذَا الدُّعَاءِ:
«رَبِّ اغْفِرْ لِي خَطِيئَتِي وَجَهْلِي، وَإِسْرَافِي فِي أَمْرِي كُلِّهِ، وَمَا أَنْتَ أَعْلَمُ بِهِ مِنِّي، اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي خَطَايَايَ، وَعَمْدِي وَجَهْلِي وَهَزْلِي، وَكُلُّ ذَلِكَ عِنْدِي، اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي مَا قَدَّمْتُ وَمَا أَخَّرْتُ، وَمَا أَسْرَرْتُ وَمَا أَعْلَنْتُ، أَنْتَ المُقَدِّمُ وَأَنْتَ المُؤَخِّرُ، وَأَنْتَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 6398]
المزيــد ...
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya kasance yana addu'a da wannan addu'ar.
"Ya Ubangiji Ka gafarta mini kuskurena da wautata, da wuce gona da irina a cikin dukkan al'amarina, da abinda Kaine Mafi sani da shi daga gareni, ya Allah Ka gafarta mini kurakuraina, da gangancina da jahilcina da kakacina, dukkan hakan daga garenin ne, ya Allah Ka gafarta mini abinda na gabatar da abinda na jinkirtar, da abinda na ɓoye da abinda na bayyana, kaine Mai gabatarwa kuma Kaine Mai jinkirtarwa, kuma kaine Mai iko akan dukkan komai".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6398]
Ya kasance daga addu'o'in Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - mai tattarowa faɗinsa:
"Ya Ubangiji Ka gafarta mini kurakuraina" da zunubina, "da jahilcina' da abinda ya afku daga gareni ba tare da sani ba.
"Da wuce gona da iri na a dukkan al'amarina" da kasawata da wuce gona da iri na.
"Da abinda Kaine Mafi sani da shi daga gareni" Ka san shi Allah ni kuma na manta shi.
"Ya Allah Ka gafarta mini kurakuraina da gangancina" da abinda ya bijiro na ganganci daga gareni da ilimi daga gareni da zunubai.
"Da (aiki) da gaske daga gareni da kakaci na" da abinda ya bijiro daga kakaci, da abinda ya afku daga gareni a hali biyun.
"Dukkanin wannan daga gareni ne" inda na tattara abinda aka ambata daga zunubai da aibuka.
"Ya Allah Ka gafarta mini abinda na gabatar" da abinda ya shuɗe, "da abinda na jinkirtar" a abinda zai zo .
"Da abinda na ɓoye" na ɓoye, "da abinda na bayyana" na bayyanar.
"Kai ne mai gabatarwa kuma Kaine Mai jinkirtarwa" Kana gabatar da wanda kake so daga halittarKa zuwa rahamarKa da dacewarKa da abinda Ka yarda da shi, kuma Kaine Mai jninkirtarwa Kana jinkirtar da wanda Kake so daga hakan da taɓarwarKa gare shi , bamai gabatar da abinda Ka jinkirtar, kuma ba mai jinkirtar da abinda Ka gabatar daga al'amura.
"Kai ne Mai iko akan dukkan komai" Mai cikakken iko Mai cikakken nufi, Mai aikata abinda Ka so.