+ -

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«اللهُمَّ أَصْلِحْ لِي دِينِي الَّذِي هُوَ عِصْمَةُ أَمْرِي، وَأَصْلِحْ لِي دُنْيَايَ الَّتِي فِيهَا مَعَاشِي، وَأَصْلِحْ لِي آخِرَتِي الَّتِي فِيهَا مَعَادِي، وَاجْعَلِ الْحَيَاةَ زِيَادَةً لِي فِي كُلِّ خَيْرٍ، وَاجْعَلِ الْمَوْتَ رَاحَةً لِي مِنْ كُلِّ شَرٍّ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2720]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cewa:
’’ Ya Allah Ka gyara mini Addini na wanda shi ne ƙashin bayan al’amari na, kuma Ka gyara mini duniya ta wacce na ke rayuwa a cikinta, Ka kuma gyara mini lahira ta wacce a cikinta ne makoma ta take, Ka sanya rayuwa (ta zamo) ƙarin duk wani alheri gareni, kuma Ka sanya mutuwa ta zamo hutu ce a gare ni daga dukkan wani sharri’’.

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2720]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - Ya yi addu'a da wata addu'a wacce ya haɗo a cikinta tushen manyan ɗabi'u waɗanda aka aiko shi dan cikasu; su ne gyara Addini, da duniya, da lahira, sai ya nemi shayarwar gyaran waɗannan abubuwan masu tattarowa guda uku a cikin wannan taƙaitaccen lafazin, sai ya fara da gyaran Addini da shi ne (za'a samu) gayaran halin gidaje biyun (duniya da lahira) sai ya ce:
(Ya Allah Ka gyara mini Addini na) shi ne Ka datar dani da tsayuwa da ladubbansa ta cikakkiyar fuska mafi cika.
(Wanda shi ne kashin bayan al'amarina) mai kiyayewa ga dukkan al'amurana, idan Addinina ya ɓaci to al'amurana sun ɓaci, na taɓe na yi asara, kuma cewa gyaruwar Addini abin nema baya cika sai da gyaruwar duniya , sai ya ce:
(Ka gyara mini duniyata) ta hanyar lafiyar jiki da aminci, da arziƙi, da mata ta gari, da zuriya kyakkyawa da abinda nake buƙatuwa zuwa gare shi, kuma ya zama na halal, mai taimako akan yi maKa biyayya, sannan ya ambaci uzuri a cikin tambayarsa gyaranta; shi ne ya ce:
(Wacce a cikinta rayuwata ta ke) da wurin rayuwata da zamanin rayuwata.
(Kuma ka gyara min lahirata wacce a cikinta ne makomata take) da komawata zuwa haɗuwa da Kai, hakan da gyaruwar ayyuka, da datarwar Allah ga bawa akan ibada da ikhalasi, da kyakkyawar cikawa.
Kuma tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya jeranta lahira bayan duniya; domin ta farko ita ce tsanin gyaran ta biyu, wanda ya daidaita a duniyarsa daidai da abinda Allah yake so, to lahirarsa ta daidaita kuma ya azirta a cikinta.
(Ka sanya rayuwa) da tsawon rayuwa (ƙari gareni a kowane alheri) da zan yawaita ayyuka na gari a cikinta. (Ka sanya mutuwa) da gaggautota (hutu gareni daga kowane sharri) da fitina da jarraba da ibtila'i da saɓo da rafkana, da kuma kuɓuta daga wahalar duniya da baƙin cikinta, da samun hutu.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية النيبالية الرومانية Oromo
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. waɗanda su ne mafi muhimancin abu; saboda haka ne Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fara addu'a da shi.
  2. Addini (shi ne) ƙashin bayan mutum da zai hana shi kowane sharri.
  3. Addu'a da al'amura na duniya saboda gyaruwar Addini da lahira.
  4. Ba'a ƙin burin mutuwa dan tsoro daga fitina a cikin Addini, ko roƙon Allah mutuwa akan shahada.