عَنِ ابنِ عُمَرَ رضي الله عنهما قَالَ:
لَمْ يَكُنْ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَدَعُ هَؤُلَاءِ الدَّعَوَاتِ، حِينَ يُمْسِي وَحِينَ يُصْبِحُ: «اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ الْعَافِيَةَ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ، اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ الْعَفْوَ وَالْعَافِيَةَ فِي دِينِي وَدُنْيَايَ وَأَهْلِي وَمَالِي، اللَّهُمَّ اسْتُرْ عَوْرَتِي -أَو: عَوْرَاتِي- وَآمِنْ رَوْعَاتِي، اللَّهُمَّ احْفَظْنِي مِنْ بَيْنِ يَدَيَّ، وَمِنْ خَلْفِي، وَعَنْ يَمِينِي، وَعَنْ شِمَالِي، وَمِنْ فَوْقِي، وَأَعُوذُ بِعَظَمَتِكَ أَنْ أُغْتَالَ مِنْ تَحْتِي».
[صحيح] - [رواه أبو داود والنسائي وابن ماجه وأحمد] - [سنن أبي داود: 5074]
المزيــد ...
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su- ya ce:
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance yana barin waɗannan addu'o'i ba lokacin da ya yi yammaci ko ya wayi gari: "Ya Allah lallai ni ina roƙonKa lafiya a duniya da lahira, ya Allah lallai ni ina roƙonKa rangwami da lafiya a Addini na da duniya ta da iyalaina da dukiyata, ya Allah Ka suturta al'aurata - ko: al'aurorina Ka amintar da tsorona, ya Allah Ka kiyayeni ta gabana, da bayana, da damana, da haguna, da samana, ina nemn tsarinKa kada a yaudareni da kisa ta ƙarƙashina".
[Ingantacce ne] - - [سنن أبي داود - 5074]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance ba yana barin waɗannan addu'o'in ba lokacin da Ya yi yammaci da lokacin da ya wayi gari:
(Ya Allah lallai ni ina roƙonKa lafiya), da kuɓuta daga masassara da masifu da tsanance-tsanance na duniya, da sha'awowi da fitintinu cikin Addini (a duniya da lahira) magaggauciya da majinkirciya.
(Ya Allah lallai ni ina roƙonKa rangwame) da shafe zunubai da ƙetare su.
(da lafiya) da kuɓuta daga aibuka, (a Addini na) daga shirka da bidi'o'i da saɓo, (da duniya ta) daga masifu da cuta da sharruka, (da iyalaina) matana da 'ya'ya na da 'yan uwana, (da dukiya ta) dukiyoyi na da aiki na.
(Ya Allah Ka suturta al'aurori na) da abinda ke cikina na aibuka da ɓaci da taƙaitawa Ka shafe zunubai na, (Ka amintar da tsorace -tsorace na) razani na da tsoro na.
(Ya Allah Ka kiyaye ni) Ka tunkuɗe bala'i daga gare ni daga abubuwa masu cutarwa da masifu, (ta gaba na da baya na, da dama na, da hagu na, da sama na) inda ya roƙi Allah Ya kiyaye shi ta kowane bangare: domin cewa masifu da aibuka kaɗai suna samun mutum ne kuma suna fuskantar sa daga ɗaya daga waɗannan ɓangarorin.
(Ina neman tsarinKa kada a kashe shi ni) shi ne a kamani bagtatan, in mutu ba tare da na sani ba (ta ƙarƙa shi na) sh ne in halaka ta kisfewa.