+ -

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمِنينَ رضي الله عنها أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَلَّمَهَا هَذَا الدُّعَاءَ:
«اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ الْخَيْرِ كُلِّهِ، عَاجِلِهِ وَآجِلِهِ، مَا عَلِمْتُ مِنْهُ وَمَا لَمْ أَعْلَمْ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ الشَّرِّ كُلِّهِ، عَاجِلِهِ وَآجِلِهِ، مَا عَلِمْتُ مِنْهُ وَمَا لَمْ أَعْلَمْ، اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ خَيْرِ مَا سَأَلَكَ عَبْدُكَ وَنَبِيُّكَ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا عَاذَ بِهِ عَبْدُكَ وَنَبِيُّكَ، اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ الْجَنَّةَ، وَمَا قَرَّبَ إِلَيْهَا مِنْ قَوْلٍ أَوْ عَمَلٍ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ النَّارِ، وَمَا قَرَّبَ إِلَيْهَا مِنْ قَوْلٍ أَوْ عَمَلٍ، وَأَسْأَلُكَ أَنْ تَجْعَلَ كُلَّ قَضَاءٍ قَضَيْتَهُ لِي خَيْرًا».

[صحيح] - [رواه ابن ماجه وأحمد] - [سنن ابن ماجه: 3846]
المزيــد ...

Daga (Nana) A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya koya mata wannan addu'ar:
"Ya Allah ina roƙon Ka dukkan alheri, magaggaucinsa da majinkircinsa, abin da na sani daga gare shi da abin da ban sani ba, kuma ina neman tsarinKa daga dukkan sharri magaggaucinsa da majinkircinsa, abin da na sani daga gare shi da abin da ban sani ba. Ya Allah ina roƙonKa mafi alherin abin da bawanKa kuma AnnabinKa ya roƙeKa, kuma ina neman tsarinKa daga sharrin abin da bawanKa kuma AnnabinKa ya nemi tsarin Ka da shi, ya Allah ina roƙonKa aljanna da abin da yake kusantota na magana ko aiki, kuma ina neman tsarinKa daga wuta, da abin da yake kusantota na magana ko aiki, ina rokonKa Ka sanya dukkan hukuncin da Ka hukunta gare ni ya zama alheri".

[Ingantacce ne] - - [سنن ابن ماجه - 3846]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya koyawa Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - dunkulallun addu'o'i su ne addu'o'i huɗu:
Na farko: Addu'a mai game kowane alheri: (Ya Allah ina roƙonKa dukkan alheri) dukkansa, (magaggaucinsa) makusanci a lokacinsa, (da majinkircinsa) na nesa, (abinda na sani daga gare shi) daga abinda Ka sanar da ni, (da abinda ban sani ba), daga abinda yake kasancewa a cikin saninKa - tsarki ya tabbatar maKa -. A cikinsa akwai fawwala al'amari zuwa ga Allah Masani Mai bada labari Mai sawwaƙawa; sai tsarki ya tabbatar maSa Ya zaɓawa musulmi maffificinsa kuma mafi kyansa, (Ina neman tsarinKa) ina neman tsarinKa ina kiyayewa (da Kai daga sharri dukkansa magaggaucinsa da majinkircinsa, abinda na sani da abinda ban sani ba).
Addu'a ta biyu: Ita ce kiyayewar musulmi daga ya yi shisshigi a cikin addu'a (Ya Allah lallai ni ina roƙonKa) ina nemanKa (daga mafificin abinda bawanKa kuma AnnabinKa ya roƙeKa) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi, (ina neman tsarin Ka) ina fakewa ina nenam tsari (da Kai daga sharrin abinda bawanKa kuma AnnabinKa ya nemi tsarin Ka) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi , wannan addu'a ce da nema daga Allah Ya bawa mai addu'ar daga abinda Annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya roƙe shi kuma ya neme shi ga kansa, ba tare da ƙididdiga nau'ikan abinda tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da shi ya roka ba.
Addu'a ta uku: Neman shiga aljanna da nisantar wuta, shi abin neman kowane musulmi ne kuma matuƙar aikinsa: (Ya Allah ina roƙon Ka aljanna) da rabauta da ita (da abinda ya kusantota na magana ko aiki) na gari wanda zai yardar da kai, (ina neman tsarinKa daga wuta) inda babu tsari daga munanan ayyuka sai da luɗufinKa, (da abinda ya kusanto zuwa gareta na magana ko aiki) daga saɓon da zai sa fushinKa.
Addu'a ta huɗu: Addu'a da yarda da hukuncin Allah (ina roƙonKa Ka sanya kowane hukuncin da Ka hukunta mini ya zama alheri) dukkan al'amarin da Allah Ya hukunta shi gareni Ya sanya shi mafi alheri gare ni, wannan yana daga addu'a da yarda da hukuncin Allah.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية النيبالية الرومانية Oromo
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Koyarwar mutum ga iyalansa abinda zai anfanar da su daga al'amuran Addini da duniya, kamar yadda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga (Nana) A'isha.
  2. Abinda ya fi ga musulmi ya haddace addu'o'in da suka zo daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; domin cewa su suna daga addu'o'i dunkulallu.
  3. Malamai sun faɗa game da wannan hadisin: Shi ne mafi tattarowar hadisai a roƙon alheri da neman tsari daga sharri, shi yana daga kalmomi masu tattarowa (kalmomi kaɗan masu ɗaukar ma'anoni masu yawa) waɗanda aka bawa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - su.
  4. Daga sabubban shiga aljanna bayan rahamar Allah: Ayyuka da kalamai na gari.