عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما قَالَ: كَانَ مِنْ دُعَاءِ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«اللهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنْ زَوَالِ نِعْمَتِكَ، وَتَحَوُّلِ عَافِيَتِكَ، وَفُجَاءَةِ نِقْمَتِكَ، وَجَمِيعِ سَخَطِكَ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2739]
المزيــد ...
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Ya kasance daga addu'ar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi -:
"Ya Allah ina neman tsarinKa daga gushewar ni'imarKa, da juyawar lafiyarKa, da shammatar azabarKa, da dukkan fushinKa".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2739]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nemi tsari daga abubuwa huɗu:
Na farko: (Ya Allah ni ina neman tsarinKa daga gushewar ni'imarKa) ta Addini da duniya kuma in tabbata akan Musulunci, in nisanci faɗawa cikin saɓon da yake gusar da ni'imomi.
Na biyu: (Da juyawar lafiyarKa) da canjata zuwa bala'i; to ina roƙonKa dawwamar lafiya, da kuɓuta daga radaɗi da cututtuka.
Na uku: (Da shammatar azabarKa) daga bala'i ko saɓo, azaba da uƙuba idan suka zo fuj'a bagtatan, to babu wani lokaci a wannan dan tuba da riska, wanda aka shafa da su zai zama mafi girma kuma mafi tsanani.
Na huɗu: (Da dukkan fushinKa) da sabubban da suke wajabta fushinKa; domin wanda Ka yi fushi da shi to haƙiƙa ya taɓe kuma ya yi asara.
Haƙiƙa tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya zo da lafazin jam'i; dan ya ƙunshi sabubban fushinSa - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - daga maganganu da ayyuka da ƙudirce-ƙudierce.