+ -

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «مَن توضأ فأحسنَ الوُضوء، ثم أتى الجمعةَ فاسْتمعَ وأَنْصَتَ غُفِرَ له ما بينه وبين الجمعة وزيادةُ ثلاثة أيام، ومَن مَسَّ الحَصا فقد لَغا».
[صحيح] - [رواه مسلم]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Wanda ya yi alwala sai ya kyautata alwala sannan ya zo Juma'a sai ya saurari huduba kuma ya yi shiru za'a gafarta masa abinda ke tsakaninsa da tsakanin Juma'a da ƙarin kwanaki uku, wanda ya taba tsakankwani to haƙiƙa ya yi yashasshiyar magana".

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 857]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wanda ya yi alwala sai ya kyautata alwalarsa da cikawa da zuwa da sunnoninta da ladubbanta, sannan ya zo sallar Juma'a kuma ya yi shiru ya karkata ga mai huɗuba, kuma ya yi shiru daga yashasshiyar magana; za'a gafarta masa ƙananan zunuban kwana goma, daga sallar Juma'a zuwa Juma'a ta biyu da ƙarin kwanuka uku; domin kyakkyawa da kwatankwacinta goma. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya gargaɗar daga rashin fuskantar zuciya ga abinda ake faɗa a cikin huɗuba na wa'azuzzuka, da kuma wasa da gabbai na shafar tsakwankwani da waninsu na nau’ukan wasa da shagaltuwa, cewa wanda ya aikata hakan to haƙiƙa ya yi yashasshiyar magana, wanda ya yi yashasshiyar magana to ba shi da rabo a cikin ladan Juma'a cikakkiya.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Yaran Tailand bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية النيبالية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwaɗaitarwa akan yin alwala da cikata da kammalata, da kiyayewa akan sallar Juma'a.
  2. Falalar sallar Juma'a.
  3. Wajabcin yin shiru a huɗubar Juma'a, da rashin shagaltuwa daga gareta da zance da waninsa.
  4. Wanda ya yi yashasshiyar magana a lokacin huɗuba to sallar Juma'ar ta yi kuma ta dauke farilla, tare da rage lada.