عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«لَا عَدْوَى، وَلَا طِيَرَةَ، وَيُعْجِبُنِي الْفَأْلُ» قَالَ قِيلَ: وَمَا الْفَأْلُ؟ قَالَ: «الْكَلِمَةُ الطَّيِّبَةُ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 2224]
المزيــد ...
Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya yarda da shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:
"Babu ciratar cuta kuma babu camfi, fatan alkairi yana birgeni" ya ce: A ka ce : Menene fatan alkairi? sai ya ce: "Magana mai dadi".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2224]
Annabi - tsira da amincin Allah agare shi - yana bada labarin cewa ciratar cutar da mutanen Jahiliyya suke ƙudircewa da cewa cuta tana cirata da kanta zuwa wani ba tare da ikon Allah ba da cewa batacce ne, (ba haka ba ne). kuma camfi batacce ne, shi ne camfi na kowanne abu, abin ji ne ko abin gani, na tsuntsaye ne ko dabbobi ko masu tawaya ko lambobi ko ranaku ko wanin hakan, kadai ya ambaci canfi ne domin cewa shi ne ya fi shahara a lokacin Jahiliyya, asalinsa shi ne sakin tsuntsu a lokacin fara wani aiki na tafiya ne ko kasuwanci ko makamancin hakan, idan ya tashi ta bangaren dama sai ya yi yunkuri ya ci gaba da abinda yake nufi, idan ya tashi bangaren hagu sai ya camfa ya ki yin abinda yake nufi. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bada labarin cewa shi fata na gari yana ƙayatar da shi, shi ne abinda yake faruwa ga mutum na farin ciki da nishadi na wata magana mai dadi da zai ji ta, ta kuma sanya shi ya dinga kyautata zato ga Ubangijinsa.