1. Gida
  2. kashe kashe

Sabuntawa Kwatankwacin tsayayye ga iyakokin Allah da mai afkawa cikinsu, kamar kwatankwacin wasu mutanene da suka yi kuri'a a jirgin ruwa, sai wasu suka samu samansa, wasunsu kuma kasansa

عَنِ النُّعْمَانِ بْنِ بَشِيرٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:

«مَثَلُ القَائِمِ عَلَى حُدُودِ اللَّهِ وَالوَاقِعِ فِيهَا، كَمَثَلِ قَوْمٍ اسْتَهَمُوا عَلَى سَفِينَةٍ، فَأَصَابَ بَعْضُهُمْ أَعْلاَهَا وَبَعْضُهُمْ أَسْفَلَهَا، فَكَانَ الَّذِينَ فِي أَسْفَلِهَا إِذَا اسْتَقَوْا مِنَ المَاءِ مَرُّوا عَلَى مَنْ فَوْقَهُمْ، فَقَالُوا: لَوْ أَنَّا خَرَقْنَا فِي نَصِيبِنَا خَرْقًا وَلَمْ نُؤْذِ مَنْ فَوْقَنَا، فَإِنْ يَتْرُكُوهُمْ وَمَا أَرَادُوا هَلَكُوا جَمِيعًا، وَإِنْ أَخَذُوا عَلَى أَيْدِيهِمْ نَجَوْا، وَنَجَوْا جَمِيعًا».

Daga Nu'uman dan Bashir - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Kwatankwacin tsayayye ga iyakokin Allah da mai afkawa cikinsu, kamar kwatankwacin wasu mutanene da suka yi kuri'a a jirgin ruwa, sai wasu suka samu samansa, wasunsu kuma kasansa, wadanda ke kasansa sun kasance idan sun nemi ashayar da su ruwa sai sun wuce wadanda ke samansu, sai suka ce: Dama a ce zamu tsaga wata kafa a rabonmu ba mu cutar da wandanda ke samanmu ba, idan sun barsu da abinda suka yi nufi za su halaka gaba dayansu, idan suka yi riko da hannayensu za su tsira, sai su tsira gaba dayansu".

الملاحظة
رائع
النص المقترح لا يوجد...
الملاحظة
التفسير مطول جدآ وغير مفهوم أنه مبهم للغايه
النص المقترح لماذا التفسير مطول للغايه ؟

Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 2493

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya buga misali ga tsayayyu akan dokokin Allah, masu tsayawa akan umarnin Allah, masu horo da aikin alheri, masu hani daga abin ki, da misalin masu afkawa dokokin Allah masu barin kyakkyawan aiki, masu aikata abin ki, da tasirin hakan a nasarar zamantakewar jama'a, kamar kwatankwacin wasu mutanene da suka hau jirgin ruwa, sai suka yi kuri'a ga wanda zai zauna a saman jirgin ruwan da wanda zai zauna a kasansa, sai wasu suka samu samansa, wasunsu kuma kasansa, wadanda ke kasa idan sun so samun ruwa sai sun wuce ta wurin wadanda ke saman, sai wadanda ke kasa suka ce: Da a ce zamu tsaga wata tsaga a daidai wurin mu a kasa mu dinga samun ruwa daga gareshi, har ya zama bamu cutar da wanda ke samanmu ba, da a ce wadanda ke sama sun barsu su aikata hakan da jirgin ruwan ya nitse da su gaba daya, da a ce sun hanasu hakan da duk jama' biyun sun tsira.

الملاحظة
الشدة مكررة مرتين عند كلمة النبي
النص المقترح لا يوجد...

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Muhimmancin horo da aikin alheri da kuma hani daga abin ki a kiyaye zamantakewar jama'a da kuma tsiransu.
  2. Daga hanyoyin koyarwa akwai buga misalai, dan kusanto da ma'anoni ga hankula kamar ga abin.
  3. Aikata abin ki a zahiri tare da kin yin inkari akansa barna ce da zata cutar da kowa da kowa.
  4. Halakar jama'a tana kasance wa ne akan barin ma'abota barna suna barna a bayan kasa.
  5. Aiki na kuskure da kyakkyawan niyya ba sa isuwa a gyaruwar aiki.
  6. Nauyin aiki a cikin jama'ar musulmi na gaba daya ne, ba'a rataya shi ga wani ayyananan mutum.
  7. Azabtar da kowa da kowa saboda zunuban wasu mutane idan ba a yi hanani ba.
  8. Masu aikata mummunan aiki suna bayyanar da mummunan aikinsu mai makon su yi alheri ga jama'a kamar munafukai.

Manufofin Fassarorin

58 Yare
EN English الإنجليزية
UR اردو الأوردية
ES Español الإسبانية
ID Indonesia الإندونيسية
UG ئۇيغۇرچە الأيغورية
BN বাংলা البنغالية
FR Français الفرنسية
TR Türkçe التركية
RU Русский الروسية
BS Bosanski البوسنية
SI සිංහල السنهالية
HI हिन्दी الهندية
ZH 中文 الصينية
FA فارسی الفارسية
VI Tiếng Việt الفيتنامية
TL Tagalog تجالوج
KU Kurdî الكردية
PT Português البرتغالية
ML മലയാളം المليالم
TE తెలుగు التلغو
SW Kiswahili السواحيلية
TA தமிழ் التاميلية
MY မြန်မာ البورمية
TH ไทย التايلندية
DE Deutsch الألمانية
PS پښتو بشتو
AS অসমীয়া الأسامية
SQ Shqip الألبانية
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча القيرقيزية
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá اليوروبا
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda الكينياروندا
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy المالاجاشية
OM Oromoo الأورومو
KN ಕನ್ನಡ الكانادا
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan الأذربيجانية
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
KMR Kurmancî الكرمنجية
kashe kashe
  • . .